An kama likitan bogi da ke ziyartar asibiti a Zamfara yana duba matsalar al’aurar mata

0
257

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara ta kama wani likitan bogi da ya bayyana kansa a matsayin likitan mata da ke aiki da asibitin ƙwararru na Yarima Bakura da ke Gusau.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Ikor Oche, a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023, ya gabatar da wanda ake zargin mai suna Muhammad Naziru Mode, bisa laifin aikata wani aiki da ya saɓawa sashi na 484 na kundin laifuffukan jihar.

Kakakin ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanan sirri.

KU KUMA KARANTA: An kama Lauyan bogi, wanda ya yi nassara a shari’o’i 26 a gaban manyan alƙalai

A cewar Oche, wanda ake zargin mai shekaru 26 wanda ya ƙira kansa “Dakta  IBB” ya ziyarci asibitin a kullum domin kula da marasa lafiya, musamman a wuraren kula da mata.

Ya ce wanda aka kama yana duba matsalolin al’aurar mata ne har da matan aure kafin dubunsa ta cika. Ya ce za a gurfanar da Likitan bogin a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply