Najeriya ta kwaso ’yan ƙasarta sama da 300 da suka maƙale a yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa tsakanin Isra’ila da mayaƙan Falasɗinawa.
Najeriya ta kwashe su ne bayan da suka tsallaka zuwa ƙasar Jordan, daga Isra’ila inda suka kai ziyarar ibada daga Jihar Legas.
Ga yadda gwamnatoci ke kwashe ’yan ƙasashensu daga Isra’ila da yankin Falasɗinawa.
An kwashe ’yan Najeriyar masu ziyarar ibada a Isra’ila ne a yayin da dubban ’yan ƙasashen waje suka maƙale a Isra’ila da Falasɗinu sakamakon yaƙin ɓangarorin da ya shiga kwana da biyar.
Aƙalla mutum dubu uku ne suka rasu, wasu kimanin dubu huɗu suka jikkata daga ɓangarorin biyu, lamarin da ya sa ƙasashe rububin kwashe ’yan ƙasashen da ke can zuwa gida.