Gwamnatin Amurka ta sanar da janye tallafin Dala miliyan 442 da take ba wa Jamhuriyar Nijar, bayan yunƙurinta na dawo da Bazoum ya gagara
Amurka ta sanar da hakan bayan da ta ayyana ƙwace mulkin da sojojin ƙasar suka yi a watan Yuli a matsayin juyin mulki.
Wani babban jami’in Amurka ya ce, ƙasarsa ta “ɗauki matakin ne saboda a tsawon wata biyu da suka gabata mun bi duk hanyoyin da suka kamata domin dawo da halastacciyar gwamnati a Nijar amma abin ya gagara.”
KU KUMA KARANTA: Rundunar sojin Faransa za ta fara kwashe dakarunta daga a jamhuriyar Nijar
Hakan na zuwa ne a ranar da rukuni na biyu na sojojin Faransa suka fice daga Nijar, tun bayan juyin mulkin da sojoji ƙarƙashin Janar Abdourahmane Tchiani suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.
Amurka da Faransa sun kafa sansanonin soji domin taimakawa wajen yaƙar ta’addanci a Nijar a zamanin Bazoum, wanda sojojin ke zargin sa da kasancewa dan amshin shatan Faransa.