Rikicin Gaza: Netanyahu na neman tayar da yaƙin duniya na uku

0
359

An zargi Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da yunƙurin haddasa yaƙin duniya na uku.

Tohon Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Farfesa Bolaji Akinyemi, ya zargi Netanyahu da nema haddasa yaƙin duniyar ta hanyar amfani da rikicin Falasɗinawa da Isra’ila don haɗa Amurka da Iran faɗa.

Farfesa Akinyemi ya yi wannan iƙirari ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Talata.

Isra’ila babbar ƙawar Amurka na zargin Iran da hannu a harin ba-zatan da ƙungiyar Hamas ta kai mata, inda ƙungiyar ta kashe aƙalla mutum 700 ta sace wasu 150.

KU KUMA KARANTA: Ana neman gangamin ba da damar shigar da kayan agaji a Gaza

Iran, wadda ke goyon bayan Hamas ta musanta zargin, a yayin da Faransa ke cewa har yanzu babu hujjar ke tabbatar da hannun Iran a harin na Asabar wanda a kansa ne Isra’ila ta mayar da martani.

An daɗe dai ana wa juna kallon haɗarin kaji tsakanin Iran da Amurka, wadda ta sha jagorantar lafta wa Iran takunkumi.

Ƙasashen duniya dai sun yi ca kan Isra’ila saboda ruwan bamabamai da ta shafe kwanaki huɗu tana yi kan Falasɗinawa a Zirin Gaza, inda ta kashe mutum sama da 700 ta rusa gidan mutane kimanin 200,000.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana yanke ruwan sha da wutar lantarki hana shigar da abinci da kuma hana shiga da fita da Isra’ila ta yi a Gaza a matsayin haramtacce.

Ko da yake Amurka da Faransa da wasu muƙarrabansu sun nuna goyon baya ga Isra’ilar.

Hukumomin agaji, ciki har da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun jaddada muhimmancin buɗe Gaza domin isar da abinci da magunguna da sauran buƙatun rayuwa a yankin da fiye da rabin al’ummarsa suka dogara da kayayyakin Jinƙai.

A halin da ake ciki kuma, hukumomi a Zirin Gaza sun ce aƙalla mutum 30 sun mutu sakamakon ruwan bama-bamai da jiragen saman yaƙi na Isra’ila suka yi a yankin cikin dare.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito kakakin Gwamnatin Zirin na Gaza, Salama Marouf, tana cewa an rusa gidaje da masana’antu da masallatai da shaguna.

Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare-hare ne a kan wuraren da matakan ƙungiyar Hamas suka ja daga.

Leave a Reply