No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kama wani matashi mai suna Goodness Oshodi mai shekaru 19 da haihuwa da ake zargin ya binne ƙaninsa mai suna Friday Oshhodi da ransa bisa zargin satar Naira 1000.

Lamarin ya faru ne da yammacin talata 10 ga watan Oktoba, 2023, a unguwar Apamisede, a ƙaramar hukumar Adavi ta jihar.

Sai dai wanda abin ya shafa ya yi sa’a da maƙwabta sun ceto shi.

A cewar shaidun gani da ido, mahaifiyar Goodness ta umarce shi da ya hukunta Friday bisa zargin satar mata Naira 1,000.

 An tattaro cewa Goodness ya lakaɗa wa Friday duka kafin ya binne shi da rai.

KU KUMA KARANTA: Ɗan fari ya kashe ɗan autansu da duka, ya raba kansa gida biyu

Da yake magana kan dalilin da yasa ya yanke shawarar binne ɗan uwansa da rai, Goodness ya ce yana aiwatar da umarnin mahaifiyarsu ne kawai da ta buƙaci ya hukunta ɗan uwansa bisa zargin satar mata Naira 1000 da ƙoƙarin gudu.

A cewarsa, mahaifiyar wadda ta umarce shi da ya hukunta Friday, ta je coci lokacin da ya binne shi da rai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP William Aya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama yaron kuma ana yi masa tambayoyi.

“Eh, muna sane.  An kama yaron, ana ci gaba da gudanar da bincike kan dalilin da ya sa kuma ta yaya hakan zai iya faruwa,” PPRO ya ƙara da cewa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...