Mutane biyu sun mutu, sakamakon rikicin manoma da makiyaya a jihar Kebbi

0
219

Rikici tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Kwanga da ke ƙaramar hukumar Ngaski a jihar Kebbi ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.

Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Abdullahi Buhari Warah ya bayyana cewa kisan da wasu mutane da ake zargin makiyaya ne suka yi wa wani manomi a gonarsa, ya kai ga harin ramuwar gayya a wani ƙauyen Fulani inda wasu fusatattun mutane suka kashe wani ƙaramin yaro, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

A cewarsa, “Faɗan ya samo asali ne sakamakon ɓarnata amfanin gona da shanu suka yi, kuma ya yi sanadin arangama, inda mutane biyu suka mutu.”

Ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya a yankin.

KU KUMA KARANTA: Rikici tsakanin ƙauyukan Osun ya sa an harbi DPO da wasu ’yan sanda huɗu

A cewarsa, ba a kama kowa ba domin manoman da makiyayan sun bar yankin ne kafin isowar jami’an tsaro.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, da aka tuntuɓe shi, ya bayyana cewa har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba.

Leave a Reply