Gwamnan Kano Abba, ya umarci a gaggauta gyara asibitin Sa-Sunusi

0
199

A ƙoƙarin sa na ingantaccen tsari a fagen ci gaban kiwon lafiya a kano kamar yadda yake ƙunshe cikin kundin manufofin sa, Gwamna Abba kabir Yusuf ya ba da umarnin a gaggauta gyara babban asibitin Sir Sunusi dake nan kano.

Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan ya bayyana haka ne jim kaɗan da kai wata ziyarar ba-zata zuwa asibitin a ƙokarin nazarin lalubo hanyoyin inganta kiwon lafiya ga al’ummar Kano.

Cikin wata sanarwa da babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai a Kano.

Gwamnan ya nuna takaici kan halin taɓarɓarewa da asibitin ya lalace, Inda nan take ya ba da umarnin fara aikin gyare gyaren domin tabbatarwa da majinyata da ma’aikatan lafiya sun samu yanayi mai kyau da ya dace a asibitin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano za ta gina gadar sama da ta ƙasa, a wasu muhimman wurare a jihar

“Tabbas ban ji daɗi kuma dole a ɗauki mataki na kawowa asibitin ɗauki, saboda abin da na gani da idona ya ban tsoro sosai da sosai, ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatin mu za ta kawo muku agaji nan ba da jimawa ba.

“Zan umurci ma’aikatar lafiya da dukkan hukumomin da ke ƙarƙashinta da su shirya yadda za a gudanar da aikin gyaran ɗakunan kwanan marasa lafiya, banɗakuna da ɗakunan yin tiyata” in ji Gwamna Abba Kabir.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a gaggauta ɗaukar wata ma’aikaciyar lafiya ta wucin gadi mai suna Khadija Adam, Saboda irin ƙwazon da take na tallafawa marasa lafiya.

Ya kuma yi wa marasa lafiya dake asibitin fatan samun sauƙi, tare da ba da kyautar naira dubu ashirin ga kowane mara lafiya da ke asibitin a matsayin tallafin gaggawa.

Leave a Reply