Hamas ta kai harin bazata a Isra’ila, ta kashe mutane 200, wasu 779 sun sami raunuka

0
156

Ƙungiyar Islama ta Falasɗinawa, Hamas ta ƙaddamar da hari mafi girma a kan Isra’ila a safiyar ranar Asabar 7 ga watan Oktoba a wani harin bazata yayin da wasu mayaƙan Hamas suka tsallaka zuwa garuruwa daban-daban na Isra’ila yayin da ake ci gaba da harba manyan rokoki daga zirin Gaza zuwa cikin Isra’ila.

A daidai lokacin rubuta wannan rahoto, an yi ta jin ƙararrakin gargaɗi (siren) a duk faɗin kudanci da tsakiyar Isra’ila, ciki har da birnin ƙudus.

Aƙalla mutane 200 ne suka mutu tun bayan da ƙungiyar Hamas ta kai harin ba-zata kan Isra’ila, in ji hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar.

An kuma jikkata wasu mutane 779 a cewar ma’aikatar lafiya ta Isra’ila.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sa-kai sun kai wa rugagen fulani hari a Sakkwato

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana kan wani mataki na yaƙi kuma ministan tsaron ƙasar ya ce ƙungiyar Hamas da ke samun goyon bayan Iran ta yi babban kuskure ta hanyar ayyana yaƙi a kan Isra’ila, a matsayin ramuwar gayya, sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare ta sama a Gaza.

Ministan tsaron Isra’ila Gallant ya ce Hamas ta ƙaddamar da yaƙi da ƙasar Isra’ila. “Sojojin Isra’ila suna yaƙar abokan gaba a kowane wuri”, in ji shi.

Harin dai ya yi nuni da kutsawa da wasu ‘yan bindigar Hamas da ba a san adadinsu ba zuwa cikin Isra’ila daga yankin Gaza, kuma ɗaya daga cikin mafi muni a rikicin Isra’ila da Falasɗinu a cikin shekaru da dama da suka gabata.

Kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun rawaito an gwabza faɗa tsakanin mayaƙan Falasɗinawa da jami’an tsaro a garuruwan kudancin Isra’ila.  

A Gaza, jama’a sun yi tururuwa don sayan kayayyaki tsammanin cewa za a iya ɗaukar kwanaki ana yaƙi a gaba.  Wasu sun fice daga gidajensu sun nufi matsuguni don samun kariya daga hare-hare.

Kwamandan sojin Hamas, Mohammad Deif ne ya sanar da fara yaƙin a wani shiri da aka watsa a kafar yaɗa labaran Hamas, inda ya yi ƙira ga Falasɗinawa a ko’ina su yi shiga yaƙin.

“Wannan ita ce yaƙi mafi girma don kawo ƙarshen mamayar da aka yi a duniya,” in ji shi, ya ƙara da cewa an harba rokoki 5,000 zuwa cikin Isra’ila.

Kafofin yaɗa labaran Falasɗinu sun rawaito cewa mayaƙan sun yi awon gaba da wasu Isra’ilawa da dama sannan kuma kafar yaɗa labaran Hamas ta yaɗa faifan bidiyo da ke nuna tankar Isra’ila da mayaƙan Hamas suka lalata.

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a jawabin da ya yi a safiyar yau ya ce ƙasar na cikin yaƙi.  Ofishinsa ya ce zai gana da manyan jami’an tsaro nan da sa’o’i masu zuwa.

Ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasɗinu ta ce mayaƙanta na tare da Hamas a harin.

“Muna cikin wannan yaƙin, mayaƙanmu suna kafaɗa da kafaɗa da ‘yan’uwansu da ke cikin dakarun Qassam Briged har sai an samu nasara,” in ji kakakin ƙungiyar Islamic Jihad Abu Hamza a wani saƙo da ya wallafa a kafar sadarwar zamani ta Telegram.

Harin dai ya zo ne kwana guda bayan da Isra’ila ta yi bikin cika shekaru 50 na yaƙin 1973 da ya kai ƙasar ga mummunan fatara a wani harin ba-zata da Siriya da Masar suka kai.

Leave a Reply