An kashe dakaru 100 a kwalejin horas da Sojoji a Siriya

0
234

Wani harin jirgi marar matuƙi da aka kai kan kwalejin horas da ƙananan sojoji a Syria ya hallaka sojoji fiye da 100, kuma tuni kafofin yaɗa labaran ƙasar suka zargi ƙungiyoyin ta’adda.

Bayanai sun ce harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin yaye ƙananan sojoji a sansaninsu da ke kan iyakar ƙasar, wanda ya kashe mutane 100, yayin da ake fargabar adadin ka iya ƙaruwa.

Wannan na zuwa ne bayan harin da Turkiyya ta kai kan mayaƙan Ƙurdawa na PKK da ya kashe mutane 9, abin da ke zama tamkar mayar da martani kan harin da ƙungiyar ta kai Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Turkiyya a farkon makon da muke ciki.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka gano gawar ɗan wasan ƙasar Ghana da girgizar ƙasa ta rutsa da shi a Turkiyya

Har yanzu dai babu wata ƙungiya ko kuma ƙasa da ta ɗauki alhakin kai wannan harin da ya rutsa har da fararen hula.

Kamfanin Dillancin Labaran Syria ya ruwaito cewa kawo yanzu harin ya yi sanadiyyar jikkata mutane kusan 200, dalili ke nan da ya sa ake fargabar adadin mamatan ka iya ƙaruwa.

Tuni kwamandan kwalejin horas da ƙananan sojojin da harin ya shafa, ya ayyana shi a matsayin rashin imani, yana mai cewa babu makawa za su mayar da martani.

Leave a Reply