No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ’yan daba sun kai hari kan wasu ‘yan sanda biyar da suka yi yunƙurin ceto wani mutum da ake zargi da satar mazakutar wani mutum a yankin Dei Dei da ke babban birnin tarayya.

An tattaro cewa ‘yan sandan da ke aiki da sashin ‘yan sanda na Gwagwa, sun je ceto mutumin da aka bayyana sunansa da Mubarak wanda ’yan daban suka kusa halaka shi a ranar Alhamis, 5 ga Oktoba, 2023.

A cewar Punch, wani mutum da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba ya yi zargin ɓacewar mazakutarsa bayan ya yi musabaha da Mubarak.

Wani mazaunin yankin da bai so a ambaci sunansa ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa ‘yan daban sun kewaye wanda ake zargin tare da lakaɗa masa duka cewa sai ya mayar wa mutumin da mazakutarsa.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sanda a Abuja sun kama mutane 14 da suka ce an sace musu mazakuta

Ya ce zuwan ‘yan sandan ya ƙara dagula lamarin ganin yadda ’yan daban maimakon su saki wanda ake zargin, sai suka far wa ‘yan sandan tare da lalata motarsu.

Kakakin hukumar ‘yan sandan Birnin Abuja SP Josephine Adeh ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an kama mutane 14 dangane da lamarin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...