Amarya da mai juna biyu sun mutu a gobarar matatar mai a Ribas

Mutane 18 sun mutu, cikinsu har da wata mai juna biyu da wata amarya, sun mutu sakamakon fashewar wata matatar man fetur ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Ribas.

Wani jami’in tsaro a yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane da dama sun ƙoƙƙone baya ga mutum 18 da suka mutu a sakamakon bindigar da matarar man ta yi.

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) a jihar, Olufemi Ayodele, ya ce, “Da tsakar dare wutar ta fara ci, inda mutane 18 suka mutu, sakamakon sun ƙone ƙurmus, wasu 25 da suka samu raunukan ƙuna kuma an cece su.Ya ce, “Yawancinsu matasa ne, sai wata mai juna biyu da wata mata da ake shirin bikin ɗaurin aurenta a cikin waɗanda a bin ya ritsa da su.”

KU KUMA KARANTA: Fashewar bututun ɗanyen mai yayi sanadiyar mutuwar mutane 12

Mazauna yakin Emohua sun ce adadin waɗanda suka mutun zai iya ƙaruwa saboda akwai waɗanda ke kwasar man da ke tafiya a ƙasa lokacin da gobarar ta tashi.

Wutar ta tashi ne bayan wuta ta kama a rumbun ajiyar mai na matatar, inda ta ƙoƙƙona mutane, ta kashe wasu.

Mazauna yakin Emohua sun ce adadin waɗanda suka mutun zai iya ƙaruwa saboda akwai waɗanda ke kwasar man da ke tafiya a ƙasa lokacin da gobarar ta tashi.
Matsalar fasa bututun mai da tacewa ba bisa ƙa’ida ba ta yi ƙamari a yankin Kudancin Najeriya, inda man da ke gangarawa ta bututun da masu satar man suke amfani da su kan yi bindiga su hallaka mutane.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *