No menu items!

Sample Page Title

Date:

Al’ummar Paris, babban birnin Faransa da sauran biranen ƙasar na fama da matsalar kuɗin-cizo yayin da ƙasar ke shirye-shiryen ɗaukar baƙuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics.

Yanzu haka ana ganin irin waɗannan ƙwari a wurare da dama a biranen.

Sai dai lamarin ya samo asali ne tun daga shekarun da suka gabata.

Wani masani kan ƙwari, Jean-Michel Berenger ya ce “a ƙarshen lokacin zafi na kowace shekara akan samu ƙaruwar kuɗin-cizo.”

KU KUMA KARANTA: Cutar mashaƙo ta kashe mutum 487 a jihar Kano

Ya ƙara da cewa “hakan na faruwa ne saboda mutane da ke yawan tafiye-tafiye a watannin Yuli da Agusta, kuma sukan kwaso su a cikin kayansu.”

Sai dai a cewarsa “yawan kuɗin-cizon da ake samu na ƙaruwa a kowace shekara.”

Yanzu haka dai gwamnatin shugaba Emmanuel Macron na buƙatar ganin an ɗauki mataki.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...