No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

A cikin wannan dare ne, al’ummar unguwar Stadium da ke garin Potiskum, suka kama mijin da ya saka wa matarsa sasari (ankwa) a ƙafa, suka miƙa shi ga jami’an tsaro.

Yadda abin ya faru shi ne, fitacciyar ‘yar kare haƙƙin ɗan’adam ɗin nan, Hajiya Fauziyya D. Sulaiman ce ta wallafa a shafinta na Facebbok, kan cewa wannan mutumi ya saka wa matarsa sasari, sannan ya hana kowa shiga gidan, hatta ‘yan’uwanta ma.

Sai aka samu wani ya lallaɓa ya je gidan, ya ɗauko hotonta da sunan unguwar. Nan take al’ummar unguwar suka cafke shi, suka miƙa shi ga hukuma. Sai zuwa gobe za a fara bincike akansa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...