Kotu ta masa ɗaurin rai-da-rai, sakamakon yi wa ’yar shekara huɗu fyaɗe a coci

0
186

Kotun sauraron laifuffukan fyaɗe da cin zarafi da ke Ikeja a jihar Legas, ta yanke wa wani mutum mai suna Ifeanyi Ndieze hukuncin ɗaurin rai da rai saboda samun shi da laifin yi wa yarinya mai shekara huɗu fyaɗe.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Abiola Soladoye, ta ce mutumin ya yi wa yarinyar fyaɗe ne a cikin coci.

Alƙalin ta ce kotun ta tabbatar da tuhumar da ake yi wa wacce ta saɓa da sashe na 261 na kundin manyan laifuffuka na jihar Legas na 2015.

Mai Shari’a Abiola ta ce yarinyar da aka yi wa fyaɗen ce ta gane mutumin da cewa ya ci mata zarafi ta hanyar cusa mata ɗan yatsa a gabanta yayin ibada a cocin.

“Daga baya an kai ta gida, amma lokacin da mahaifiyarta ta yi mata wanka, sai ta ga tana zubar da jini babu ƙaƙƙauta wa. A asibitin ne likitoci suka ba da shawarar a kai batun gaban ’yan sanda.

KU KUMA KARANTA: Wani Dattijo ya yi wa yarinya kurma fyaɗe ta mutu

“Wannan mutumin tataccen maƙaryaci ne, kuma kotu ta san shi da aikata laifin, don haka ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai,” in ji alƙalin.

Tun da farko, lauyar gwamnati, Olufunke Adegoke, ta shaida wa kotun cewa an aikata laifin ne a cocin da ke kan titin Salau Street, ranar 29 ga watan Oktoban 2020.

Leave a Reply