’Yan sa-kai sun kai wa rugagen fulani hari a Sakkwato

0
194

’Yan sa-kai sun kai wa rugagen Fulani hari bayan ’yan bindiga sun kashe mutum uku sun sace wasu a ƙaramar hukumar Binji ta jihar Sakkwato

Wani mazaunin ƙauyen Soro, ya ce, Da misalin ƙarfe 1 na daren Litinin ne dandazon ’yan bindigar suka far wa ƙauyen “da garken dabbobin da sake zargin sun sato ne daga wasu ƙauyuka.

“A nan ƙauyen kuma sun kashe mutum uku, suka jikkata wasu uku sannan suka sace wasu da dama, cikin har da iyalan wani gida gaba ɗayansu.

“Bayan nan ne ’yan sa-kai da muke da su suka kai hari rugagen Fulani da ke kusa da mu suka kashe wasu mazaje daga cikinsu suka ƙona bukkokinsu.”

Shaidan namu ya ce, “akwai raɗe-raɗin cewa Fulanin sun yi wani taro kafin harin da aka kawo mana, mutanenmu na zargin a wannan zaman ne Fulanin suka shirya hari da aka kawo mana, saboda an jima ana zaman doya da manja tsakaninmu da su.”

KU KUMA KARANTA: Hukumar DSS a Kano ta kama wata mata kan yunƙurin harin ƙunar baƙin wake

Ya ce, “Yanzu haka wasu mutane sun tsere saboda tsoron harin ɗaukar fansa,” amma wata majiyar ta ce ƙurar ta lafa bayan da aka tura jami’an tsaro yankin.

Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato ASP Ahmad Rufa’i ya shaida wa Aminiya cewa, “’yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Soro amma sojoji da ’yan sanda sun fatattake su.

“Duk da haka ’yan bindigar sun ƙona wasu gidaje, inda a sanadiyyar haka suka kashe mutum uku, wasu kuma suka samu raunuka.

“An kai harin ɗaukar fansa amma jami’anmu sun shawo kan lamarin bayan zama da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Kaigama ya yi da shugabannin ƙauyukan.

“Kwamishinan ya girke motocin sintiri guda huɗu a yankin domin tabbatar da doka da zaman lafiya,” in ji jami’in.

Leave a Reply