’Yan sanda a Abuja sun kama mutane 14 da suka ce an sace musu mazakuta

0
229

’Yan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun kama wasu mutane 14 da suka ce an sace musu mazakuta.

A cewar ’yan sandan, zargin da mutanen suka yi ya sa wasu fusatattun mutane sun ɗauki doka a hannunsu ta hanyar hukunta waɗanda aka shafa wa kashin kajin a daidai lokacin da matsalar take daɗa ƙaruwa a birnin.

Kwamishinan ’yan sanda mai kula da yankin babban birnin, Haruna Garba, ne ya bayyana hakan a hedikwatar ’yan sandan da ke Abuja, yayin da yake jawabi ga ’yan jarida ranar Talata.

Ya ce an kama mutanen ne saboda sun ba jama’a da ’yan sanda bayanan ƙarya, yana mai cewa aikinsu ne kare rayuka da dukiyoyin mutane.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Yobe sun kama gawurtaccen ɓarawon katin cirar kuɗi

Haruna ya kuma ce, “Mutum sha huɗun da suka yi da’awar an sace musu mazakutar mun kai su asibiti, inda likitoci suka tabbatar da cewa babu abin da ya samu mazakutar tasu, kuma tana aiki.

“A kan haka ne muka gurfanar da su a gaban kotu saboda yaɗa bayanan ƙarya da kuma tayar da hankalin jama’a.

“Ina kuma shawartar mazauna Abuja da su ja kunnen ’ya’yansu da su guji yaɗa irin waɗannan ƙarairayin sannan su guji ɗaukar doka a hannunsu,” in ji Kwamishinan ’yan Sandan.

Leave a Reply