’Yan bindiga sun kashe kansila a Katsina

0
207

’Yan bindigar sun kashe Samaila Buhari Mairago a yayin da yake shirin gudanar da aikin sintiri a matsayinsa na ɗaya daga cikin jami’an samar da tsaro.

Shaidu sun ce ’yan bindigar sun kashe Kansilan gundumar Nasarawa, Hon Samaila Buhari Mairago ne bayan dawowarsa daga ofishin ’yan sanda inda ya karɓo bindiga domin gudanar da sintiri a matsayinsa na ɗaya daga cikin jami’an samar da tsaro da gwamnatin jihar ta horas.

Wani maƙwabcinsa, Malam Musa Maibulo, ya ce bisa alama maharan sun shigo yankin ne da nufin sace wani, amma tsautsayi ya faɗa kan kansilan a daren na Litinin.

Malam Musa ya ce, “babu wanda ya lura, kowa na gudanar da harkokinsa ba tare da sanin cewa ɓata-garin sun shigo ba.

KU KUMA KARANTA: Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutane 52 a wurin Maulidi a Pakistan

“Kansilanmu Samaila Buhari wanda ke cikin masu sintiri ya je ofishin ’yan sanda na Maƙera ya ɗauko bindigarsa domin aikin sintiri yadda suka saba, amma aka yi rashin sa’a, ya je shiga gidansa, sai ’yan bindigar suka lura da bindigar da yake rataye da ita, shi ne suka buɗe masa wuta,” suka ɗauke bindigar suke tsere nan take.

Ya ce sai “bayan tserewarsu ne muka gane cewa sun sace wani maƙwabcinmu mai suna Malam Samaila Maikatako.”

Wani kawun mamacin, Abbas Isma’il wanda ya ce marigayin ya bar mace ɗaya da ’ya’ya takwas, ya ce, “Abin takaici ne yadda ’yan bindiga suka addabi garin Funtuwa.

“Ko a ranar 3 ga watan Agusta sai da suka sace wata fitacciyar mai sayar da abinci, Hajiya Fati Mai Waina, kuma har yanzu ba su sako ta ba.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce rundunar ta samu rahoton abin da ya faru kuma tana gudanar da bincike a kai.

Leave a Reply