Hukumar DSS a Kano ta kama wata mata kan yunƙurin harin ƙunar baƙin wake

Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS, ta kama Fiddausi Musa Ahmadu, mai shekaru 23, bayan ta yi barazanar kashe kanta tare da kashe duk waɗanda ke da alhakin nasarar jam’iyyar ‘All Progressives Congress’ (APC), ɗan takarar gwamna a Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.

Jaridar Alfijir ta rawaito  wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da kama Fiddausi Musa Ahmadu.

KU KUMA KARANTA: Hukumar DSS a Nasarawa, ta kama jami’an NASEMA bisa zargin karkatar da kayan abinci

A cikin faifayin bidiyo, an ji Fiddausi tana cewa za ta kai wa babban alƙalin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna hari, inda ta yi gargaɗin cewa duk inda ta gan ta, ba za ta damu da riƙe ta da bom.

Hakazalika, Fiddausi wanda ke sanye da jar hula, ta gargaɗi Nasiru Yusuf Gawuna ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC da cewa, “ka da ka kuskura ka bayyana inda kake, in ba haka ba, ba na damu da buga maka rigar bama-bamai .

Haka kuma na kai wa mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima hari, inda ta ɗora masa laifin dambarwar jam’iyyar NNPP a Kano.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *