No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rahoton jaridar ‘The Nation’ na cewa hare-haren da jiragen yaƙin sojojin saman Najeriya (NAF) suka kai sun kashe ‘yan ta’adda da dama da ke yin sintiri a yankin tafkin Chadi na jihar Borno.

Harin na sama ya kuma lalata maɓoyar ‘yan ta’addar, da gine-gine, da kuma  maɓoyarsu.

Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, 2 ga Oktoba.

Ya ce an far wa ‘yan ta’addan ne a wuraren da suke Tumbun Fulani da yankin Tumbun Shitu da ke gaɓar tafkin Chadi daga ranar 27 zuwa 30 ga watan Satumba.

KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta kama maɓoyar ‘Yahoo-Yahoo’ a Benuwe, ta kama mutane 14 da ake zargi

Kakakin NAF ya ce hare-haren ta sama ya zama wajibi ne bayan da sojoji suka tabbatar da ayyukan ‘yan ta’addan “ya zama barazana ga tsarin soja da ‘yan Najeriya masu bin doka da oda da ke zaune a wuraren.”

Gabkwet ya ce: “A Tumbun Fulani, an ga ‘yan ta’adda suna loda jarkoki a cikin manyan motoci biyu da aka ɓoye a ƙarƙashin bishiyoyi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...