Gwamnatin Iran ta yi afuwa ga fursunoni 1,000 albarkacin ranar Maulidi

0
110

Gwamnatin Iran ta yi afuwa a sama da fursunoni 1,000 daga gidajen yarin ƙasar domin murnar bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW).

Wata kafar yaɗa labarun gwamnati ta ce an kuma sassauta hukuncin kisa da aka yanke wa mutane 54.

Dama dai jagoran addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenie kan yi afuwa ga fursunoni a lokutan murna na addinin musulunci daban-daban.

Leave a Reply