An kama wani tsoho ɗan shekara 70 mai suna Anthony Mgbenwa Okpara da laifin yi wa wata yarinya kurma mai shekaru 13 fyaɗe ta mutu har lahira a jihar Enugu a ƙauyen Aborjieze da ke yankin Umuagu-Inyi mai cin gashin kansa a ƙaramar hukumar Oji ranar 23 ga watan Satumba.
A cewar mazauna yankin. Yarinyar mai suna Uche, ta rasu ne bayan da wanda ake zargin ya yi lalata da ita.
“Gawar yarinyar tana cikin ɗakin ajiyar gawa yayin da muke magana kuma muna son a tantance wannan al’amari a cikin dokar da ta dace don zama kange ga sauran masu aikata laifuka,” wata majiya ta shaida wa jaridar The Sun.
KU KUMA KARANTA: Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta
Wanda ake zargin wanda aka kama bayan an kai rahoto ga ‘yan sanda, yanzu haka yana tsare a hedikwatar ‘yan sandan jihar Enugu.
Mazauna unguwar sun ce sun ƙuduri aniyar ganin an yi wa yarinyar adalci domin yarinyar kurma ce, kuma iyayenta na fama da talauci, saboda mai yiwuwa wanda ake zargin ya so ya yi amfani da kuɗi domin lalata lamarin kafin a kai shi gaban kotu.