Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar rushe-rushen shagunan ‘yan kasuwa a jihar

0
188

Wata babbar kotun tarayya ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar naira biliyan 30 ga ‘yan kasuwar da ta ruguza wa shaguna a Filin Babban masallacin Idi na Kano a watannin baya.

Mai shari’a S. A. Amobeda na babbar kotun tarayyar ne ya bayar da umarnin a wani hukunci da ya yanke ranar Juma’a.

Waɗanda suka kai ƙarar sun haɗa da ‘yan kasuwa da masu shaguna da masu gidaje da ‘yan tebura a filin idin ƙarƙashin wata ƙungiya da ake ƙira Masallacin Idi Shop Owners Association kamar yadda Dakta Nuruddeen Ayagi, lauyan ‘yan kasuwar ya shaida wa BBC.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da hukuncin har ma ta ce za ta ɗaukaka ƙara.

Lauyan ‘yan kasuwar ya ce kotun ta ce rushe-rushen da gwamnatin Kano ta yi wa ‘yan kasuwa a filin Idin ya haddasa ɓarnar da ta kai naira biliyan 250.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta hana gwamnatin Kano rushe gine-gine a hanyar Jami’ar Bayero Kano

“Kotu ta ce lailai gwamnatin Kano ta biya ‘yan kasuwa diyyar naira biliyan 30 saboda girman ɓarnar da aka yi musu, da cin zarafi da cin mutuncinsu.” in ji lauyan

Ya kuma ce kotun ta hana gwamnatin jihar sayar wa wani filayen da ta rushe, ko a cikin Najeriya ko daga wajen Najeriya har abada.”

Lauyan ya ƙara da cewa kotun ta kuma umarci gwamnatin kano ta mayar wa ‘yan kasuwar da ta rusa wa shaguna da filayensu.

Sai dai lauyan gwamnatin jihar wanda kuma shi ne kwamishinan shari’a, Barister Haruna Deideri ya ce hukuncin babbar kotun tarayyar ba karɓaɓɓe ba ne.

Ya ƙara da cewa dokar mallakar ƙasa ta bai wa gwamna cikakken iko a kan ƙasa a ko ina take a cikin jihar da yake mulki.

“Mu har yanzu muna ganin mai girma gwamna bai aikata wani abu da ya saɓa wa doka ba, saboda haka yana da ikon da zai ɗauki matakin da zai amfani al’ummar Kano.”

Leave a Reply