Gwamnatin ƙasar ta ce za ta fitar da sanarwar ranar da za a sake buɗe makarantun.
Fiye da makarantu 56,000 aka rufe a ƙasar Pakistan, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar ciwon ido mai saurin yaɗuwa, in ji jami’an ƙasar a ranar Laraba.
Miliyoyin ɗalibai ne dai za su zauna a gida daga ranar Alhamis bayan da yankin Punjab, lardin da ya fi yawan jama’a a ƙasar, ya ba da sanarwar rufe makarantu.
Hakan dai ya biyo bayan kamuwar da mutum 357,000 suka yi da cutar tun farkon shekarar nan.
Ciwon ido da ke saurin yaɗuwa yana sanya ido ya yi ja, yana sanya zazzaɓi da zubar da jini daga idanu kuma cutar na iya yaɗuwa ta hanyar haɗa hannu, da kuma tari ko atishawa.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Pakistan tara sun mutu, sakamakon hare-haren ‘yan Taliban
Kakakin Ma’aikatar Ilimi ta Punjab Zulfiqar Ali, ya shaida wa AFP cewa “An sanar da rufe makarantun a matsayin wani mataki na samar da kariya ga ɗalibai daga kamuwa da cutar.”
Akwai mazauna 127,000,000 a gabashin lardin Punjab da makarantun jiha 56,000, da kuma dubunnan makarantu masu zaman kansu su ma sun rufe.
“Muna fatan wannan zai karya tasirin kamuwa da cutar a lardin,” in ji Ali.
An riga an rufe makarantu a duk faɗin Pakistan a ranar Juma’a har zuwa lokacin da gwamnatin a ƙasar za ta fitar da sabuwar sanarwa
Hukumomin Punjab sun ce za a tantance ɗaliban a ƙofar makaranta idan sun sake buɗe makarantun nan gaba.