Daga Ibraheem El-Tafseer
Jami’an tsaron sirri a Burkina Faso sun daƙile yunƙurin juyin mulki da wasu suka yi a ƙasar, a cewar gwamnatin mulkin sojin ƙasar.
Gwamnatin na zargin cewa wasu jami’ai sun shirya kawo ruɗani a ƙasar da kuma jefa ta cikin tashin hankali.
Hakan ya zo ne kasa da shekara guda da karɓe ikon mulkin ƙasar da shugaba Ibrahim Traoré ya yi.
Juyin mulkin da aka yi a ƙasar a 2022, shi ne na biyu da aka samu, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar ayyukan masu iƙirarin jihadi.
Wata sanarwa da hukumomi suka karanta a gidan talabijin ɗin ƙasar da yammacin ranar Laraba, sun ce sun kama wasu mutane, kuma suna ci gaba da neman wasu, sai dai ba su bayar da wani ƙarin bayani ba.