‘Yan sanda a Ekiti sun cafke waɗanda suka kashe wani mai POS, suka sace miliyan uku

0
323

Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta kama wasu mutane 13 da ake zargin ‘yan ƙungiyar asiri ne da suka kashe wani ma’aikacin POS mai suna Olasunkanmi Joseph tare da kwashe masa kudi Naira miliyan uku da dubu ɗari biyar a Ado-Ekiti.

Ku tuna cewa an kashe Olasunkanmi a Irona Roundabout da ke Ado Ekiti da rana tsaka a ranar Alhamis, 6 ga Afrilu, 2023, yayin da yake dawowa daga banki.

An gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar rundunar a ƙarshen mako tare da wasu mutane 16 da aka kama bisa zargin aikata laifuka daban-daban kamar su garkuwa da mutane, da kuma yunƙurin kisa.

KU KUMA KARANTA: An cafke Kwamishinan ‘yan sanda na bogi a Legas

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sunday Abutu, ya ce an kama waɗanda ake zargin ‘yan ƙungiyar asiri ne bayan da aka samu labarin cewa suna shirin sake kai wani harin fashi da makami daga maɓoyar su.

Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu na kasancewa mambobin ƙungiyar asiri ta Supreme Eiye Confraternity a Ikere-Ekiti kuma suna da hannu wajen kai hare-hare na fashi da kuma garkuwa da mutane.

A cewar PPRO, bindigar AK-47 da aka samu daga hannun waɗanda ake zargin na daga cikin makaman da aka yi amfani da su wajen kashe ma’aikacin POS.

Leave a Reply