DSS ta kama babban Editan jaridar Almizan a filin jirgin sama na Kano

0
457

Daga Ibraheem El-Tafseer

Iyalan Babban Editan Jaridar ALMIZAN, Malam Ibrahim Musa sun yi ƙira ga Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS da su gaggauta sakinsa.

Wannan ƙiran ya fito ne a wata takardar manema labarai da iyalan Editan suka fitar, wanda Abdullahi Usman ya sa wa hanu.

Sanarwar ta ce; “muna sanar da an ɗauke babban Editan jaridar Almizan, Malam Ibrahim Musa wanda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka yi”, in ji sanarwar.

Jaridar ALMIZAN, jaridar Hausa ce wadda take fito wa mako-mako da ake bugawa a Kaduna.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; jami’an tsaron sirri na Nijeriya wato DSS ne suka yi awon gaba da Ibrahim Musa wanda ke tare da wata ‘yar uwarsa Binta Sulaiman a filin jirgin sama na Aminu Kano da sanyin safiyar ranar Laraba a kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji na Umrah.

“A halin da ake ciki dai, babu wani dalili da hukumomi suka bayar na kama shi duk da cewa ya shahara tare da ba da gudumawa wajen ƙiran a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda aka kama bayan kisan gillar da sojoji suka yi na kusan mutum 1000 na mabiyansa da gwamnatin Nijeriya ta yi a shekarar 2015 a Zariya ta jihar Kaduna”, in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: An kama ɓarayin da suka fasa shago suka saci wayoyin hannu 996 da kwamfuta tara

Sanarwar ta ƙara da cewa; “Yana daga cikin masu kamfen ɗin da ya yi sanadin samun hukuncin babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin a saki Shaikh Zakzaky da kuma biyan diyya ga jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, wanda ake kyautata zaton jami’an tsaron da suka yi rashin nasara a shari’ar ba su ji daɗi ba”.

“Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama musamman Amnesty International sun matsa wa tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasiru Elrufai wanda ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatinsa ta binne mutane kusan 350 da aka kashe a wani kabarin bai ɗaya a ƙauyen Mando da ke Kaduna”, in ji sanarwar.

“An dai san Ibrahim Musa a matsayin ɗan gwagwarmaya mai fafutika tare da tofa albarkacin bakinsa game da ayyukan ta’addanci na ƙasa, kashe-kashen ba bisa ƙa’ida ba, da kuma mayar da wasu tsiraru musulmi saniyar ware da gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta yi.

“Ya sanya ransa a cikin hatsar domin tabbatar da an yi adalci kan dubban waɗanda aka kama sakamakon kisan gillar da gwamnati ta yi wanda aka tursasa wa gwamnati ta saki waɗanda ta kama ta hanyar amfani da hanyoyin shari’a.

“Muna ƙira da a gaggauta sakin Malam Ibrahim Musa cikin aminci wanda laifinsa kawai shi ne ya tsaya kan ƙin amincewa da kisan kiyashi da rashin bin doka da oda da masu riƙe da madafun iko ƙarƙashin gwamnatin Buhari ke yi.

“Muna kuma son jawo hankalin hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki kan illar da ke tattare da tsawaita ayyukan kashe-kashen da gwamnatin da ta shuɗe ta yi na ba gaira ba dalili, zuwa ci gaba da hakan a gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu.

“Muna so mu yarda da cewa wannan gwamnati mai ci ta Bola Tinubu ba za ta so ta bayyana kanta a matsayin mai cin zarafin tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba, take haƙƙin bil’adama da kuma tsoratarwa ta hanyar kisan ƙare dangi da gwamnatin da ta shuɗe ta yi.

“A don haka muna ƙara jaddada ƙiran a gaggauta sakin sa ba tare da wani sharaɗi ba”, sanarwar ta ƙarƙare.

Leave a Reply