Kenya ta sha alwashin kawo ƙarshen yaƙin Gang na Haiti

0
286

Kenya ta ce tana da ƙwarin gwiwar tura ɗaruruwan ‘yan sandanta zuwa Haiti nan da watan Janairu zai kawo ƙarshen yaƙin da ake yi na ‘yan ƙungiyar a can.

A shekarar da ta gabata gwamnatin Haiti ta nemi taimako saboda ta’addancin ƙungiyoyin da ke ƙara ruruwa.

Ƙungiyoyin dai sun yi galaba a kan ‘yan sanda kuma yanzu haka suna da iko da fiye da kashi uku cikin huɗu na babban birnin ƙasar.

Da farko jami’an Kenya sun yi magana game da jami’ai kusan 1,000 da za su je Haiti don horar da ‘yan sandan yankin da kuma taimaka wa wajen kare muhimman cibiyoyi a wurin.

Sai dai ministan harkokin wajen Kenya Alfred Mutua ya ce za ta kasance rundunar shiga tsakani don kwance ɗamarar abin da ya ƙira ‘yan daba.

KU KUMA KARANTA: Yankunan da ake tafka yaƙi a Sudan sun ƙara yawa

A wata hira da BBC Alfred Mutua ya ce ‘yan sandan Kenya za su kuɓutar da ‘yan Haiti da aka yi garkuwa da su tare da ‘yantar da matan da ake yi wa fyaɗe.

Ya ce bai yi tsammanin za a yi tashin hankali ba. Wasu sun nuna shakku game da tura jami’ai mai nisan kilomita 12,000 (mil 7,500) zuwa Haiti.

Musamman ganin yadda ake fama da ƙalubalen doka da oda a Kenya kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun daɗe suna zargin ‘yan sanda da aikata ta’asa da suka haɗa da kashe-kashe da azabtarwa.

Leave a Reply