Wata matashiya a jihar Abiya, ta kashe mahaifiyarta ta hanyar sa mata guba a abinci

0
219

Wata ‘yar shekara 12 mai suna Precious Okome, daga Nchara Oloko a Ikwuano, jihar Abiya, ta bayyana cewa ta gano maganin kashe ƙwari a banɗakinsu, sannan ta ɗiga a cikin abinci mahaifiyarta da ta rene ta wato Misis Stella Iheanacho.

An tambayi ɗalibar JSS1 na makarantar sakandaren Ibeku dalilin da ya sa ta yi hakan, sai ta ce wani mutum mai suna Ijele da ya yi magana da ita a cikin barci ya ce ta sanya wa matar guba.

Da aka tambaye ta ko za ta ci abinci mai guba da take tsammanin mahaifiyarta ta ci, sai ta amsa da rashin fahimta.

Leave a Reply