‘Yan sanda a Taraba sun kama mutane 20 bisa zargin garkuwa da mutane

0
206

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta ce ta kama wasu mutane 20 bisa zargin yin garkuwa da mutane a faɗin jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Usman ya ce, sun kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri da samun ƙorafe-ƙorafe wajen jama’a dangane da ayyukan masu garkuwan, da suka addabi sassan jihar.

Abdullahi Usman, ya ce duka mutanen sun amsa zargin da ake yi musu.

Ya ce jami’ansu suka ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da kuma wata ƙaramar bindiga harba ka ruga.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da likita a Kogi

A cewarsa, mutanen da ake zargin sun karɓi sama da naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa daga iyalan waɗanda suka sace wa ‘yan uwa.

“Rundunar ‘yan sandan ba ta ja da baya ba a ƙoƙarinta na ci gaba da farautar ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka a jihar bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun,” in ji shi.

Usman ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta ƙaddamar da farautar ‘yan ta’adda a wasu wuraren da suka fi zafafa ayyukansu, musamman ma a Jalingo, babban birnin jihar.

Leave a Reply