‘Yan sanda a Borno sun kama tubabben ɗan Boko Haram ɗin da ya kashe tsohuwar matar sa

0
251

‘Yan sanda a jihar Borno sun kama wani Musa Dauda, ​​tubabben ɗan Boko Haram da ake zargin ya kashe tare da binne tsohuwar matarsa, Hafsat Musa, a wata gona da ke filin wasa na Muhammed Goni, Maiduguri.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Sani Kamilu, ya bayyana haka a Maiduguri a ranar Juma’a, inda ya ce, Dauda ya gayyaci Hafsat mai shekaru 45 da haihuwa domin ta gana da shi a gonarsa da ke harabar filin wasa, ranar 12 ga watan Satumba.

Kamilu ya bayyana cewa Hafsat ba inda take bayan ta amsa wannan gayyata.

Mista Kamilu ya ƙara da cewa “Ba a kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda ba sai bayan ‘yan kwanaki bayan da ‘yan uwanta suka gano gawar Hafsat da ta lalace a gona.”

Ya bayyana cewa ‘yan sandan sun ɗauki matakin ne nan take; ya ziyarci inda lamarin ya faru tare da kwashe gawar Hafsat zuwa asibitin Umaru Shehu Ultramodern dake Maiduguri domin a tantance gawarwakin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Kaduna, sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da huɗu

Mista Kamilu ya kuma bayyana cewa an kama Mista Dauda ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba kuma ya amsa laifin aikata laifin.

Ya ƙara da cewa Mista Dauda ya ce ya ga Hafsat tare da wani a gona sai ya daka mata fartanya a kai kafin ta faɗi ta mutu.

Daga baya Mista Dauda ya binne Hafsat a gona ya gudu, in ji Kamilu. Mista Kamilu ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban ƙuliya manta sabo.

Leave a Reply