An kama ‘yan ‘Yahoo Boys’ 28 da aka samu da laifin zamba a Anambara

0
228

A ƙalla ‘yan ‘Yahoo Boys’ 28 ne aka yankewa hukunci bisa laifin zamba a jihar Anambara.

Kakakin Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Mista Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a Abuja.

Uwujaren ya bayyana cewa, “Mai shari’a Nnadi O. Dimgba na babbar kotun tarayya da ke zaune a Awka, jihar Anambra a ranar Talata, 19 ga Satumba, 2023, ya yanke wa wasu ‘yan damfara ta intanet 28 hukunci a kan wasu tuhume-tuhume daban-daban da suka haɗa da aikata laifuka da yunƙurin samun kuɗi ta hanyar ƙarya.

“Waɗanda ake tuhuman da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙi Tu’annati (EFCC) ta shiyyar Enugu ta gurfanar da su, Emmanuel Chidozie Katchi, Chukwudi ThankGod Chiazor, Chinonso Raymond, Ejike Moses Ezeoma, Okafor Silas, Akuh Stanley Chidera, David Franklin Orobo, Emmanuel Chisom Orizu, Uche Ejidike, Ezechukwu Casmir Chibuokem, Nwanolue Godswill, Nnadi Collins Arinze.

Sauran su ne, Kemelu Valentine Obinna, Chukwuebuka Augustine Onyemaobi da Chukwuemeka Emmanuel Ajaegbo. “Sauran su ne Ebuka Peter Obinyo, Shedrack Ezekiel Aaron, Israel Chibueze Chibuike, Kingdom Princewill Ameachi, Ezeh Goodness Makachukwu, Victor Chukwubuikem Hezikiah, Anyidiaso Lotanna Patrick, Somtochukwu Valentine Ezeobi, Asouzu Francis Chukwuma, ThankGod Chimaijem Obioma da Chukwuemeka Kingsley Ireka.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a jihar Yobe sun kama wasu da ake zargi da fashi da makami a jihar

“Dukkan su sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su, an kuma yanke musu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kowanne daga ranar 19 ga Satumba, 2023.

Amma an ba su zaɓin tarar da hidimar al’umma don tsaftace harabar babbar kotun tarayya a cikin bayanan da suka shafi batun.

EFCC Enugu Command.” Uwujaren ya ƙara da cewa kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsu yayin da aka bayar da umarnin a miƙa su ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Leave a Reply