Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeria (NDLEA) a ranar Laraba a Owerri ta tabbatar da kashe jami’anta biyu tare da wasu jami’an tsaro uku a ranar Talata a yankin ƙaramar hukumar Ehime-Mbano da ke Imo.
Kwamandan NDLEA a Imo, Abubakar Wali ya shaida wa manema labarai cewa an kashe kowane jami’in sojan saman Najeriya, ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaro da na farar hula a harin.
Ya ƙara da cewa kowane jami’in hukumar NDLEA da na sojojin ruwan Najeriya guda ɗaya ya samu raunuka sakamakon harbin da aka kai musu, kuma suna karɓar magani a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya dake Owerri.
Wali ya ce ma’aikatan na rundunar ‘Forward Operation Base’ ne, rundunar tsaro da ta ƙunshi jami’an rundunar sojin Najeriya da kuma hukumar shige da fice ta Najeriya.
KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA a Kaduna, ta tarwatsa haramtattun gidajen ƙwayoyi 13
Ya ce an ƙona motocin jami’an tsaron ne yayin da aka kwashe makamai da alburusai na jami’an da suka mutu, duk da cewa an ƙwato bindigar ta NDLEA.
“Abin takaici ne yadda muka rasa jami’ai biyu sannan muka samu ɗaya da rauni. “Ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a kama waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya,” in ji Wali.
Shima da yake magana a kan wannan mumunan kisa, gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana takaicin yadda jami’an tsaro da ke taimaka wa wajen binciken laifukan da suka aikata a jihar ana kai hari.
Ya kuma buƙaci mazauna ƙauyukan da ke kewaye da su ba da kai bayanai masu amfani da za su kai ga cafke maharan da suka gudu zuwa ga hukumomin tsaro.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Mohammed Barde, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a wurin da harin ya faru, ya ce maharan sun yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna ne a hanyar Obowo-Ehime Mbano.
Ya ƙara da cewa maharan sun yi harbin bindiga tare da harbin bama-bamai kan jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikinsu.