‘Yan bindiga a jihar Imo sun kashe sojoji takwas

Wani mummunan lamari ya auku a jihar Imo yayin da Jaridar Vanguard ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun kashe soji takwas, ‘yan sanda da jami’an NSCDC a wani ƙazamin kwanton ɓauna da suka yi masu.

Vanguard ta rawaito a ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka kai hari tare da kashe jami’an tsaro a ƙalla takwas, tare da ƙona motoci biyu a jihar Imo.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe a Oriagu, daura da reshen Aba da ke ƙaramar hukumar Ehime Mbano a jihar Imo.

Jami’an tsaron da abin ya shafa dai sun haɗa da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya na Najeriya, NSCDC.

Bidiyon harin da aka kai, ya nuna gawarwakin sojoji kusan huɗu waɗanda ba su da rai a cikin kakinsu da bindigogi.

Haka kuma motocinsu guda biyu suna ci da wuta.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

A lokacin da ake gabatar da wannan rahoto, an ce an ba da kariya ga titin da ta isa wurin da lamarin ya faru.

Tashin hankali ya ci gaba da gudana a ciki da wajen al’ummar da abin ya shafa.

A cewar ganau, “Al’amarin ya faru ne kimanin sa’o’i biyu da suka wuce.  Da farko na ga motocin Hilux guda biyu a lokacin da suka taso daga Oriagu sun nufi reshen Aba da ke Ehime Mbano.

“Kamar yadda nake magana da ku yanzu motocin Hilux na ci gaba da cin wuta ‘yan bindigar sun ƙona sojojin.

“Tashin hankali yana ko’ina.  Mun rufe shagunanmu, mu je gida, muna ganin jami’an tsaro da yawa, sun tare hanya, mutane suna gudu zuwa gidajensu jama’ar mu na fargabar komai na iya faruwa a yanzu.

“Motar farko, na ga sojoji sama da biyar.  A na biyu kuma na ga jami’an tsaro sama da huɗu.  Sun ce an kashe su duka.”

Har ya zuwa lokacin miƙa wannan rahoton, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo, PPRO, Henry Okoye, bai mayar da martani kan binciken ba.


Comments

One response to “‘Yan bindiga a jihar Imo sun kashe sojoji takwas”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a jihar Imo sun kashe sojoji takwas […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *