Ana ci gaba da gudanar da laifukan cin zarafin ɗan’adam a Habasha – Majalisar Ɗinkin Duniya

0
314

Ƙwararru kan kare hakkin bil adama na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce ana ci gaba da aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil adama a sassa daban-daban na ƙasar Habasha watanni 10 bayan da dakarun gwamnati da na yankin Tigray suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Rahoton nasu ya bayyana halin da ake ciki a ƙasar Habasha a matsayin mummunan yanayi.

Tana tattara laifukan da kowane ɓangare suka aikata, ciki har da sojojin Eritrea – a lokacin yakin Tigray.

KU KUMA KARANTA: Cin zarafi ne, canza wa yara halittar fata – Likitan fata

Hukumar kula da kare haƙƙin bil adama ta ƙasa da ƙasa kan ƙasar Habasha ta ce dakarun gwamnati na kamawa da tsarewa da azabtar da fararen hula a Oromia.

Har ila yau, ta bayar da rahoton samun rahotannin sahihanci da yawa na cin zarafi da aka yi wa farar hular Amhara tun bayan ayyana dokar ta ɓaci a can a watan jiya.

Leave a Reply