An tashi baran-baran tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadago

0
326

A ranar litinin ne aka kawo ƙarshen taron gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), ba tare da cimma matsaya kan buƙatun ƙungiyar ba.

Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong; da ƙaramin Ministan ƙwadago da Aiki, Nkeiruka Onyejeocha, ya gana da Shugaban NLC, Joe Ajaero, da sauran shugabannin a Abuja a ƙoƙarin da suke na hana ƙungiyoyin ƙwadagon yin wani aikin masana’antu.

Ana sa ran ci gaba da taron nan gaba kaɗan. Sai dai kuma ana sa ran ministan zai yi wata ganawa da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (TUC) a yau.

Rikicin ya biyo bayan gayyatar da Lalong ya yi wa ƙungiyar NLC domin gudanar da wani taro dangane da yajin aikin da ƙungiyar ke shirin yi a faɗin ƙasar sakamakon cire tallafin man fetur da kuma wahalhalun da ƙasar ke fuskanta.

KU KUMA KARANTA: Kungiyar Kwadago Ta Gargadi Gwamnatin Jihar Kaduna Kan Tsoma Baki A Harkokin Ta

Tun da farko dai, ministan ya gayyaci ƙungiyoyin NLC da kuma TUC domin tattaunawa don daƙile yajin aikin na kwanaki biyu da aka gudanar tsakanin 5 zuwa 6 ga watan Satumba.

Duk da haka, “TUC ne kawai ya halarci taron,” in ji ma’aikatar. A yayin taron na ranar Litinin, Lalong ya yi alƙawarin yin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙwadago don magance buƙatun ƙungiyoyin ƙwadagon bisa adalci da daidaito.

Ya yi ƙira ga shugabannin ƙwadago da su kasance masu gaskiya da gaskiya a cikin tattaunawar.

Ministan ya kuma bayyana fatansa na ganin taron zai kai ga cimma matsaya mai amfani ga ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply