Al’ummar Okanla da ke jihar Osun, wani mummunan lamari ya auku a ranar Lahadin da ta gabata yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaƙi fadar Olokanla na Okanla.
A yayin harin an kashe wani mai neman shiga jami’a mai suna Ibrahim Qudus, inda maharan suka ci gaba da cinnawa ginin fadar da wata mota wuta.
Da yake zanta wa da jaridar PUNCH Metro, kawun marigayin, Jimoh Qadri, ya bayyana cewa maharan ƙarƙashin jagorancin wani mutum mai suna Naim, ba su rufe fuskokinsu ba, sai dai shi kansa Naim.
Qadri ya bayyana ruɗani game da dalilin da ya sa aka kai harin amma ya yi hasashen hakan na iya kasancewa da alaƙa da rikicin filaye a yankin.
Qadri ya bayyana cewa, maharan sun bi ni ne, sun yi ta leƙa a cikin gidan, inda ba su same ni ba, sai suka lalata ginin, suka wuce gidan iyalina, inda mahaifina mai suna Olokanla na Okanla ya kasance a matsayin fadarsa.
KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo
A can ne suka ga Qudus, ɗan ƙanina, wanda yake zaune a Ibadan, har ya zuwa kwanan nan ya dawo gida neman shiga jami’a, bayan ya rubuta UTME, aka kashe shi, suka sa gawarsa a cikin motata da aka ajiye a cikin harabar gidan, suka ajiye motar, motar ta ƙone, sun kuma ƙona fadar.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni Kwamishinan ‘yan sandan ya ziyarci wurin.
An kuma tura ƙarin jami’an tsaro domin hana tashe tashen hankula a yankin. Iyalan waɗanda suka mutu suna roƙon a kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika, kuma suna ƙira ga jami’an tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin hukunta su.