Jami’an tsaron ‘Civil Defence’ na Najeriya reshen jihar Osun, a ranar Juma’a, sun gurfanar da wani matashi ɗan shekaru 40 a duniya bisa zarginsa da karɓan kuɗi har Naira miliyan 13 da sunan sayar da filaye biyar a wani.
Wanda aka damfara ɗin mai suna Samuel an yi masa alƙawarin filaye biyar a yankin Ikorodu da ke jihar Legas bayan ya biya miliyan 13.
Kwamandan NSCDC na Osun, Sunday Agboola, yayin da yake gabatar da wanda ake zargin, ya ce an biya kuɗaɗen ne a bagaje daga 2019 zuwa 2023.
A cewar Agboola, ” Matakin ya ci karo da sashe na 419 na dokar laifuka da kuma sashe na zamba da sauran laifukan da suka shafi zamba na 2006.”
KU KUMA KARANTA: Hukumar NSCDC a Kwara ta gurfanar da mutane biyu kan zargin fyaɗe
Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin ya ce ya karkatar da kuɗin ɗan uwansa ne don yin wasu kasuwanci amma kasuwancin ya ci tura.
“Mun rigaya mun biya kuɗin filin amma mai filin ya mayar mini da kuɗin cewa an samu matsala a filin.
Na yanke shawarar yin amfani da kuɗin don kasuwanci kafin in mayar wa ɗan uwana. “Na yi amfani da kuɗin wajen sayan shanu daga arewa amma harkar ta ci tura.
Ban yi nufin in kwashe kuɗin ɗan uwana ba kuma a shirye nake in biya idan aka ba ni lokaci.”
Agboola ya bayar da tabbacin cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan karewar binciken.
[…] KU KUMA KARANTA: Hukumar NSCDC a Osun, ta kama wani mutum bisa zargin zambar miliyan 13 […]