Gwamna Yobe ya ba da tallafin kuɗi a mutane 1000 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

3
264

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya ƙaddamar da tallafin kuɗi Naira dubu ɗari (N100,000) kowane ga kimanin mutane 1000 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin jihar a ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na ‘COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus’ (NG-CARES).

Wannan shiri na NG-CARES shiri ne wanda ake aiwatar da shi tsakanin gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi.

“Har ila yau, shirin NG-CARES wata hanya ce mai inganci wanda zai ƙara wa ƙoƙarin gwamnatin jihar Yobe wajen aiwatar da shirinta na farfaɗo da yankunan da ayyukan ‘yan ta’adda ya shafa a jihar, musamman fannin ayyukan yi da samar da kuɗaɗen shiga da kuma dogaro da kai.” Inji Gwamnan.

Gwamna Buni ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bayar da gudumawar sama da Naira biliyan 1.8 domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare daban-daban na shirin NG-CARES.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin guda tara

Gwamna Buni ya ƙara da cewa, “waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da manoma, ƙananan ‘yan kasuwa da matsakaita haɗi da samar da ƙananan ayyukan yi sama da 44 ga yankunan karkara sama da 21 da ke ƙarƙashin hukumar FADAMA da ci gaban al’umma da sauran shirye-shirye masu alaƙa da shi.”

Bugu da ƙari kuma, Gwamna Buni ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin tarayya, abokanan arziƙin jihar Yobe, ƙungiyoyin bayar da agaji don kawo wa jihar ci gaba da sauran abubuwan da suka shafi tallafi wa rayuwa da ci gaban jihar.

3 COMMENTS

Leave a Reply