Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Gwale

0
303

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Gwale Khalid Ishaq Diso na tsawon watanni uku bisa zargin sayar da kadarorin gwamnati.

Zargin da ake yiwa Diso ya fito ne daga kansilolinsa.  Kwamitin riƙo na majalisar kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu ne ya gabatar da rahoton a zaman taron da shugaban majalisar, Alhaji Isma’il Jibril Falgore ya jagoranta.

Alhaji Hamza Zubairu Massu ya bayyana cewa kwamitin ya yi nazari sosai kan zarge-zargen da ke ƙunshe a cikin ƙarar da ‘yan majalisar Gwale 6 daga cikin 10 suka shigar.
Zarge-zargen da ake yiwa shugaban da aka dakatar sun haɗa da sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba da kuma ɗaukar mataki ba tare da tuntuɓa ba.

Majalisar ta umurci mataimakin shugaban majalisar da ya karɓi ragamar tafiyar da harkokin majalisar har sai an kammala bincike.

Leave a Reply