Mutane sama da dubu biyu ne suka mutu a Libya, sakamakon ambaliyar ruwan sama

2
313

Daga Ibraheem El-Tafseer

Yawan mutanen da suka mutu sanadin ambaliyar ruwa a ƙasar Libya ya ƙaru zuwa sama da 1,500 a birni guda ɗaya kawai, a cewar ministan da ya kai ziyara Derna, birnin gaɓar teku.

“Na kaɗu game da abin da na gani, tamkar ambaliyar tsunami,” Hisham Chkiouat, daga gwamnatin da ke sansani a gabashin ƙasar, ya ce.

Ruwa ya shafe mafi yawan sassan birnin Derna, wanda matsuguni ne ga mutane kimanin 100,000, bayan madatsun ruwa guda biyu da gadoji huɗu suka karye.

Sama da mutum 10,000 ne aka ba da rahoton cewa sun ɓata bayan gawurtacciyar guguwar da aka yi laƙabi Daniel ta auka, kamar yadda ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ba da rahoto.

KU KUMA KARANTA: Akwai barazanar ambaliyar ruwa a jihohi takwas a Najeriya – NEMA

Guguwar wadda ta auka wa ƙasar ranar Lahadi, ta kuma shafi biranen gabashin Libya, kamar Benghazi da Soussa da Al-Marj.

Hashem Chkiouat, ministan sufurin jiragen sama kuma ɗan kwamitin kai ɗauki na gwamnatin gabashin ƙasar ya faɗa wa BBC cewa karyewar ɗaya daga cikin madatsun ruwan da ke kudancin Derna, ya sa ruwa ya janye sassan birnin zuwa cikin teku.

Adadin mutanen da suka mutu gaba ɗaya, mai yiwuwa ne zai ƙaru fiye da haka.

“Ban zuzuta maganata ba, idan na cewa kashi ɗaya cikin huɗu na birnin ya ɓace. Gidaje da yawa, masu yawa nake faɗa muku, sun ruguje.”

Biranen gabashi irinsu, Benghazi da Sousse da kuma Al-Marj, su ma duk abin ya shafe su.

Tun da farko, Firaministan Osama Hamad ya faɗa wa wata tashar talbijin ɗin Libya cewa sun ƙiyasta mutane kimanin 2,000 ne suka mutu yayin da wasu dubbai kuma suka ɓace: “Unguwanni gaba ɗaya a birnin Derna sun ɓace, tare da mazaunansu… duka ruwa ya awon gaba da su.”

Tare da sauran yankunan gabashin ƙasar, birnin Misrata da ke yammacin Libya na cikin sassan da ambaliyar ruwan ta aukawa.

Ruwan sama ya haddasa mummunar ambaliya tare da zaftarewar ƙasa da kuma lalata gidaje da tituna da dama.

An ayyana yankin Derna a matsayin wanda mummunan bala’i ya aukawa, sannan an yi shelar zaman makoki na kwana uku.

Bayanai sun nuna cewa abu ne mai wuya a iya bayyana yawan mutanen da suka halaka, saboda babu hanyoyin sadarwa sosai.

Sannan kuma ga rashin tartibiyar gwamnati, sakamakon yaƙin da aka kwashe wajen shekara goma ana yi, tsakanin manyan abokan gaba biyu a ƙasar.

Sojojin ƙasar ta Libya bakwai ne aka bayar da rahoton sun ɓace a lokacin da suke gudanar da aikin agaji.

Jami’ai a gabashin ƙasar da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin da ƙasashen duniya ba su amince da ita ba sun ayyana dokar hana fita, yayin da suka bayar da umarnin rufe makarantu da shaguna.

An sa dokar hana fita da kuma makoki na kwana uku a gabashin ƙasar

Masana sun yi gargaɗin cewa sauyin yanayi na duniya na nufin za a samu ƙaruwar tururi a lokacin bazara, wanda hakan zai haddasa mamakon ruwan sama da iska.

A yanzu mahaukaciyar guguwar mai tafe da mamakon ruwan saman ta isa yammacin Masar.

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce za ta tura jiragen sama uku da za su kai ma’aikatan agaji da kuma kayan taimako zuwa ƙasar ta Libya.

Tun shekara ta 2014 Libya ke ƙarƙashin mulkin abokan gabar biyu bayan kashe daɗaɗɗen shugaban ƙasar Muammar Gaddafi a 2011.

Gwamnatin Firaminista Fayez al-Serra wadda ke samun goyon bayan majalisar ɗinkin duniya na yaƙi da tawayen Janar Khalifa Haftar wanda ƙasashe da hukumomin duniya ba su amince da mulkinsa ba kuma yake riƙe da iko a yankin gabashin ƙasar.

2 COMMENTS

Leave a Reply