Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wani kwamishinan ‘yan sanda na bogi.
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamun a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba, yayin da yake yiwa manema labarai ƙarin haske kan nasarorin da rundunar ta samu a baya-bayan nan.
Ya ce an kama wanda ake zargin “CP na jabu”, mai suna Emmanuel, a ranar 2 ga Satumba, da misalin ƙarfe 4:40 na yamma a lokacin da ya ziyarci rundunar ‘yan sanda a yankin Ikorodu kuma ya gabatar da kansa a matsayin kwamishinan ‘yan sanda.
KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC
“An martaba shi, amma da aka tambaye shi, an gano shi kwamishinan jabu ne. A yayin bincike a gidansa, mun gano katin shaidar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Kenwood walkie-talkie, camouflage na ‘yan sanda, singlet da hular fuska na yan sanda,” inji shi.