A sama mana sana’ar yi – Tubabbun ‘yan Boko Haram

0
210

Tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram sun yi ƙira ga gwamnati da ta samar musu da hanyoyin rayuwa yayin da suke sake tsugunar da su cikin al’ummomin da aka yi musu gyara.

A lokacin da take zantawa da ‘News Point Nigeria’ kaɗai a cibiyar farfaɗo da Bulumkutu da ke Maiduguri inda ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, Betta Edu ta raba musu kayan abinci da kuma wasu ‘yan matan Chiɓok da aka ceto, tsoffin ‘yan ta’addan sun bayyana damuwarsu kan halin da suke ciki a halin yanzu, inda suka ƙara da cewa wasu daga cikinsu suna tunanin komawa daji.

“Har yanzu ina zaune a sansanin duk da cewa hukumomi sun sako ni amma ba ni da inda zan je, yawancin mu ba su da aiki har wasu na tunanin komawa daji.

“Ni mai gyaran walda ne kuma mai gyaran bindigu a Sambisa, lokacin da nake miƙa wuya na kawo bindigu biyar a matsayin gudunmawata ga gwamnatin Najeriya,” in ji ɗaya daga cikin tubabbun mayaƙan Boko Haram, Ali Kaka.

Wani tubabbun mayaƙan Boko Haram, Suleiman Abubakar, ya ce, “Ni ɗaya ne daga cikin waɗanda suka miƙa makamansu kuma na yi hakan ne saboda na gaji da kashe-kashe da sata kuma ina buƙatar fara sabuwar rayuwa.

KU KUMA KARANTA: Boko Haram a Borno sun yi garkuwa da mata bakwai, sun kashe biyar

“Mun ɗauki makami ne saboda rashin aikin yi ko kuma tabbatacciyar hanyar rayuwa don haka zan roƙi gwamnati da ta samar mana da hanyar rayuwa ta yadda wasun mu da suka miƙa wuya da gaske ba za su sake gwadawa ba.”

Yayin da yake mayar da martani ga roƙon nasu, Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya tana bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta rage raɗaɗin talauci a tsakanin talakawa a cikin al’umma ta fara samar da tallafi da rance mai sauƙi wanda nan ba da daɗewa ba za a fara.

Duk waɗanda suka tuba da ceto ‘yan matan Chiɓok da sauran su sun taru a yawansu domin tarbar ministar.

Cibiyar farfaɗo da Bulumkutu ita ce ake ajiye waɗanda aka ceto da suka haɗa da ‘yan matan makarantar Chiɓok da tubabbun ‘yan tada ƙayar baya domin sa ido da tantance su kafin a sake shigar da su cikin al’umma.

Leave a Reply