‘Yan Najeriya miliyan 11 ne ke samun wutar lantarki – NBS

0
221

Adadin masu amfani da wutar lantarki ya ƙaru da 200,000 daga miliyan 11.27 a rubu’in farko na shekarar 2023 zuwa miliyan 11.47 a rubu na biyu na shekara.

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, (NBS), ta bayyana a cikin rahotonta na wutar lantarkin Najeriya na kashi na biyu na shekarar 2023 da aka fitar a Abuja ranar Juma’a cewa ƙarin ya kai kashi 1.84 cikin ɗari.

Rahoton ya mayar da hankali ne kan lissafin makamashi, kuɗaɗen shiga da ake samu, da kuma abokan cinikin kamfanonin rarraba wutar lantarki a lokacin da ake nazari.

Ya bayyana cewa a duk shekara adadin masu amfani da wutar lantarki ya ƙaru da kashi 6.17 a kashi na biyu na shekarar 2023 daga miliyan 10.81 da aka ruwaito a daidai lokacin a shekarar 2022.

Ya ƙara da cewa, a cikin kwata na biyu na shekarar 2023, yawan abokan hulɗar mitoci ya kai miliyan 5.47 daga miliyan 5.31 da aka rubuta a rubu’in farko na shekarar, wanda ya ƙaru da kashi 3.10 cikin ɗari.

KU KUMA KARANTA: Majalisar Bauchi ta buƙaci da a gyara na’urorin lantarki da suka lalace

“A duk shekara, wannan adadi ya ƙaru da kashi 10.40 cikin 100 daga adadin miliyan 4.96 da aka ruwaito a kwata na biyu na 2022,” in ji NBS.

Hakazalika, ƙiyasin abokan cinikin wutar lantarki sun kai miliyan shida a kashi na biyu na shekarar 2023, wanda ya nuna ƙaruwar kashi 0.72 cikin ɗari sama da masu amfani da wutar lantarki miliyan 5.96 da aka samu a rubu’in farko na shekarar.

Dangane da shekara-shekara, ƙiyasin abokan ciniki sun ƙaru da kashi 2.58 a cikin kwata na biyu na 2023 daga miliyan 5.85 da aka yi rikodin a daidai lokacin a cikin 2022.

NBS ta kuma bayyana cewa, kamfanonin rarraba wutar lantarki sun tara kuɗaɗen shiga na Naira biliyan 263.08 a kashi na biyu na shekarar 2023, adadin da ya ƙaru fiye da Naira biliyan 247.33 da suka tara a rubu’in farko.

Ya ƙara da cewa a duk shekara, kuɗaɗen shiga da aka tara sun ƙaru da kashi 39.63 bisa ɗari sama da Naira biliyan 188.41 da aka tara a rubu’i na biyu na shekarar 2022.

Ya bayyana cewa wutar lantarki ta ƙaru zuwa 5,909 (Gwh) a rubu na biyu na shekarar 2023 daga 5,851 (Gwh) da aka samu a rubu’in farko na shekarar.

NBS ta ƙara da cewa a duk shekara ana samun ƙaruwar wutar lantarki da kashi 13.06 a kashi na biyu na shekarar 2023 idan aka kwatanta da 5,226 (Gwh) da aka ruwaito a rubu na biyu na 2022.

Leave a Reply