Ya kashe kakarsa mai shekara 100, saboda ba zai iya kula da ita ba

A ranar Alhamis ne aka zargi wani mutum da kashe kakarsa mai shekaru 100 da gatari yayin da take zaune a kan keken guragu.

Ana ci gaba da shari’a a birnin Hamburg da ke arewacin Jamus bisa zargin kisan kai.

“Ba zai iya jure kula da ita ba,” lauya mai shigar da ƙara ya shaida wa kotu.

Lauyan da ya shigar da ƙara ya bayyana yadda wanda ake tuhuma, ɗan ƙasar Jamus mai shekaru 37, haifaffen Estonia, ya kai wa matar hari a gidanta na Hamburg da sanyin safiyar ranar 6 ga watan Maris.

Matar da ke fama da ciwon hauka, ta samu sara da gatari, a ƙalla a wurare 16 a kai da wuyanta yayin da take ƙoƙarin kare kanta.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Kaduna, sun kashe ‘yan bindiga huɗu, sun kama 13

A cewar mai gabatar da ƙara, ta faɗi ƙasa ta karye a kafaɗarta.

Ta rasu ne sakamakon raunukan da ta samu a ƙashin bayanta.

Wanda ake zargin ya ƙira hukumar bayar da agajin gaggawa ta wayar tarho da kansa inda ya ce ya kashe kakarsa, wacce ta mutu lokacin da ‘yan sanda suka isa wurin.

Mutumin ya ba da kansa ba tare da gardama ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *