Gwamnatin Zamfara ta zuba jami’an tsaro a wasu muhimman wurare a jihar

1
319

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauki matakin zuba jami’an tsaro a manyan hanyoyin da ke fuskantar barazanar ‘yan bindiga.

Idan ba a manta ba, a zaman Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara wanda aka gudanar makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya yi ƙorafi ga shugabannin ɓangarorin tsaro na jihar kan wasu hanyoyi da ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka. Musamman hanyar Gusau zuwa Funtua; Magami zuwa Ɗangulbi zuwa Ɗan Kurmi zuwa Anka, da kuma hanyar Magami zuwa Ɗansadau.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwar manema labarai da ya fitar yau a Gusau, ya ce, zuba jami’an tsaro a hanyar Gusau zuwa Funtua da sauran hanyoyi na daga cikin shirin gwamnatin don tabbatar da kawo ƙarshen matsalar tsaro.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya yaba wa jami’an tsaro wajen ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a jihar

Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron da ke sintiri a waɗannan hanyoyi sun haɗa da sojojin ƙasa, sojojin sama da ‘yan sanda.

Ya ce: “A taron Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara wanda aka yi makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya nemi shugabannin sojoji da ‘yan sanda su tura motoci masu silken a CSK da APC domin yin sintiri a muhimman hanyoyin da ‘yan bindiga ke ta’asa.

“Haka kuma gwamnan ya yi wa shugabannin jami’an tsaron alƙawarin duk wani tallafi da suke buƙata don yiwuwar aikinsu ba tare da wata tangarɗa ba.

“Cikin matakan da gwamnatin Dauda Lawal ke ɗauka don magance wannan masifa ta rashin tsaro ne ya sa ta bayar da umurnin a rufe wasu kasuwanni da ake amfani da su wurin cinikayyar shanu da tumakin sata.”

1 COMMENT

Leave a Reply