Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin shanu takwas

0
197

Gwamnatin Zamfara ta sanar da rufe kasuwannin shanu guda takwas nan take a ƙananan hukumomi biyar na jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Mannir Haidara ya fitar ranar Lahadi a Gusau.

Ya ce majalisar tsaron jihar ta amince da rufe kasuwannin shanu na wucin gadi yayin taron da ta gudanar a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta.

A cewarsa matakin na daga cikin matakan tunkarar sabbin hare-hare da satar shanu a sassan jihar.

“An ɗauki matakin ne biyo bayan sake ɓullar satar shanu da ake yi a yankunan da lamarin ya shafa.

“Kasuwannin shanun da abin ya shafa su ne: Danjibga da Kunchin-Kalgo a Tsafe; Kasuwan shanu na Bagega da Wuya a garin Anka. “Sauran su ne Dangulbi da Ɗansadau a Maru, Dauran a Zurmi da Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyim,” in ji Kwamishinan.

KU KUMA KARANTA: Likitoci a Zamfara sun dakatar da shiga yajin aiki

Haidara ya ce majalisar ta ɗorawa hukumomin tsaro da hukumar kula da lafiyar dabbobi da kiwo, da su tabbatar da bin doka da oda.

Ya jaddada ƙudurin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na maido da zaman lafiya a jihar.

Leave a Reply