Mutum biyu sun mutu, biyar sun jikkata a hatsarin mota a Ondo

1
196

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ondo ta ce mutane biyu sun mutu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka a wani hatsarin da ya faru a daren Juma’a a unguwar Olokuta da ke kan hanyar Akure zuwa Ondo.

Ezekiel Son Allah, kwamandan hukumar FRSC a jihar, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya aukuwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Asabar.

Mista Son Allah, wanda ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:48 na yamma, ya ce hatsarin ya rutsa da manya maza shida da mace baliga ɗaya.

Kwamandan sashin ya alaƙanta musabbabin hatsarin, wanda ya haɗa da motar kasuwanci guda ɗaya da kuma mota ƙirar Honda Accord da ke gudu.

“A ranar Juma’a da misalin ƙarfe 5:48 na yamma a unguwar Olokuta Correctional Centre da ke kan titin Akure-Ondo, wata mota ƙirar Nissan Primera mai lamba FGB-96XA da kuma motar Honda Accord mai lamba MUS-834 AL sun yi hatsari.

KU KUMA KARANTA: Ma’aikatan jirgin ƙasa biyar sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Italiya

“Samari biyu sun mutu nan take, yayin da manya maza huɗu da babba mace ɗaya suka samu raunuka.

“An ajiye waɗanda suka mutu a ɗakin ajiye gawa na asibitin ƙwararru na jihar Ondo da ke Akure, yayin da aka miƙa motocin ga ‘yan sanda,” inji shi.

Mista Son Allah ya hori masu ababen hawa da su riƙa bin ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa, inda ya ce duk wani abu da ya saɓa wa doka za a kama shi kuma a hukunta shi.

1 COMMENT

Leave a Reply