Sojojin Pakistan tara sun mutu, sakamakon hare-haren ‘yan Taliban

0
178

Wani ɗan kunar baƙin wake ya kashe sojoji tara ta hanyar kutsawa da babur ɗinsa cikin wata motar sojoji a arewa maso yammacin Pakistan.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai wa sojojin a bana, kamar yadda jami’ai suka bayyana a ranar Juma’a.

Wasu sojoji biyar kuma sun jikkata a harin da aka kai cikin dare a gundumar Bannu, wani ƙaramin gari da ke maƙwabtaka da yankin Waziristan da ke kusa da kan iyakar Afghanistan.

Yankin dai ya taɓa riƙe hannun mayaƙan Islama masu alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda.

Sanarwar da sojoji suka fitar a yammacin jiya Alhamis ta ce sojojin sun killace yankin bayan tashin bam ɗin tare da neman waɗanda suka kai harin.

KU KUMA KARANTA: Taliban ta hana matan Afghanistan fita karatu a UAE

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai waɗannan hare-hare na baya-bayan nan, sai dai ƙungiyar Taliban ta Pakistan da ƙungiyar IS na kai hare-hare kan jami’an tsaro da fararen hula a yankin.

‘Yan Taliban na Pakistan, waɗanda suka rabu da takwarorinsu na Afganistan duk da cewa dukkansu suna bin tsarin Islama mai tsaurin ra’ayi iri ɗaya, sun kashe dubban mutane a irin waɗannan hare-hare a cikin shekarun da suka gabata.

An fatattake su daga yankunan da suke da ƙarfi a kan iyakar Afghanistan a wani jerin hare-hare tun shekara ta 2014.

Sun yi ta neman sake haɗuwa bayan faɗuwar Kabul ga hannun ‘yan Taliban na Afghanistan a 2021.

Leave a Reply