No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Ruqayya Mukhtar a ranar Alhamis ta shaida wa wata kotun Shari’a da ke zamanta a Rigasa, Kaduna cewa mijinta ya yi shekara biyu bai kwanta da ita ba.

Mai shigar da ƙarar da ta roƙi a raba aurenta da wani Naziru Hamza ta kuma koka da yadda mijinta ya ci zarafinta da cin mutunci.

Akan karewarsa, wanda ake tuhumar ya musanta dukkan zarge-zargen inda ya ce ya yi iya ƙoƙarinsa wajen gamsar da matarsa ​​ta hanyar jima’i.

“Tunda na fita neman abincin yau da kullum, wasu lokuta nakan dawo gida a makare kuma a gajiye amma matata ba ta fahimta, koyaushe tana cewa sai na kusance ta.

KU KUMA KARANTA: ‘Mijina ya ƙi yin aiki, ya zauna tare da ni a gidan mahaifina’

“Nakan wajabta sau da yawa kuma a wasu lokuta ina roƙon ta da ta yi haƙuri har sai da safe kuma ba na dukanta” in ji shi.

Alƙali Anass Khalifa ya tambayi mai ƙarar ko tana da shedu sai tace eh.

Ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 5 ga watan Satumba domin mai karar
ta gabatar da shaidunta.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...