Gwamnan Gombe ya ba da umarnin rufe dukkan gidajen ‘Gala’ da ke jihar

0
133

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya CON ya bayar da umarnin rufe dukkanin gidajen ‘Gala’ da ke cikin jihar nan take.

Sakataren Gwamnatin Jiha, Farfesa Ibrahim Abubakar NJoɗi, wanda ya ba da sanarwar umarnin, ya ce ana samun ƙorafi daga mutanen gari, akan irin rashin tarbiyyan da ake aikatawa a wajen.

Don haka Gwamnan ya umarci ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya da kuma Operation Hattara da su tattara jami’ansu domin aiwatar da wannan umarni tare da tabbatar da bin doka da oda.

KU KUMA KARANTA: A guji bin hanyar Bauchi zuwa Gombe saboda rugujewar gada – FRSC

Domin kaucewa shakku, gidajen Gala da abin ya shafa su ne: Jami’a Gidan Wanka dake Mile 3 Road, Gombe, gidan wasan kwaikwayo na White House (Babban Gida) dake New Mile 3 Road Yola Road, Gombe; Gidan Lokaci General Merchant dake Mile 3 Reservoir Road, Gombe and Farin Gida Entertainment II dake Wuro Karal, Kalshingi Road, Gombe. Sauran sune: Gidan Zamani Entertainment New Mile 3, Yola Road, Tumfure, Gombe; Albarka Entertainment Dake Wuro Karal, Bypass kusa da Hara Form, Gombe; Gidajen Gala Suna Garin Kuri, ƙauyen Lubo da ƙauyen Kurba duk a cikin ƙaramar hukumar Yamaltu Deba.

Haka kuma abin ya shafa akwai Tauraren Wash dake Trailer Park, Bauchi Road, Gombe da Gidan Gala dake cikin Garin Bajoga a ƙaramar hukumar Funakaye.

Leave a Reply